ABNA24 : Mataimakiyar Shugaban kasar Samia Suluhu Hassan ce ta sanar da mutuwar shugaban a gidan talabijin din kasar.
A cewar mataimakiyar shugaban, Mista Magufuli ya rasu ne da yammacin ranar Laraba a asibitin Mzena da ke Dar es Salaam sakamakon ciwon zuciya.
Nan gaba a cewar mataimakiyar shugaban kasar, za’a gudanar da jana’izarsa, sannan kuma an ayyana zaman makoki na kwanaki 14 domin alhinin mutuwar Magufuli.
Dama dai marabin da a ga shugaban kasar bainar jama’a tun karshen watan Fabarairu da ya gabata, sakamakon larurar dake damunsa.
Ya kuma shafe fiye da shekara 10 yana fama da larurar.
Bisa kundin tsarin mulkin Tanzaniya, za a rantsar da mataimakiyar shugaban kasar ce ,domin karasa wa’adin shekaru biyar din da ya rage.
An dai sake zabar John Magufuli ne a matsayin shugaban kasar ta Tanzaniya, a watan Oktoban shekarar 2020.
342/